Koma Labarai
Labarai

Har yanzu ba mu soke sana'ar "Downloading" ba a Kano - Hukumar Tace Fina-finai

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Har yanzu ba mu soke sana'ar "Downloading" ba a Kano - Hukumar Tace Fina-finai

Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta jihar Kano, ta ce har yanzu ba ta sanar da soke sana'ar tura fina-finai (Downloading" ba a faɗin jihar Kano.

Wannan na cikin sanarwar da jami'in yaɗa labarai na Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis 16 ga Yuli, 2026.

Sanarwar ta ce biyo bayan korafe-korafen da Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano ta karɓa daga masu sana'ar tura fina-finai"downloading" da shugabanninsu, sakamakon wani rahoto da ke yawo cewa an haramta ko an soke sana'ar tasu a faɗin Jihar Kano, Hukumar ta gudanar da cikakken nazari tare da bayyana matsayarta akai.

Hukumar ta ce babu wata hukuma da ta tuntuɓi, ko ta yi shawara da Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano kafin ɗaukar irin wannan mataki.

A cewar sanarwar, "Masu sana'ar "downloading" na daga cikin masu ruwa da tsaki da Hukumar ke da alhakin sa ido kan ayyukansu bisa tanadin dokar data kafa Hukumar, tare da ɗaukar matakin ladabtarwa idan aka samu wanda ya karya ƙa'idojin gudanar da sana'ar"

Hakazalika ta ce har zuwa wannan lokaci, Hukumar ba ta karɓi wani ƙorafi a hukumance ba, sai dai ta gano wani saƙon murya da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke bayyana wani salon rashin da'a da ake zargin wasu daga masu Sana'ar "downloading" ke yi, na tura bidiyon tsaraici cikin wani salo na ɓadda bami.

Sanarwar ta ce nan take Hukumar ta fara gudanar da bincike, inda sakamakon farko ya nuna cewa muryar da ke cikin saƙon ana zargin ba daga Jihar Kano take ba, amma duk da haka, bincike na ci gaba da gudana domin gano haƙiƙanin gaskiyar lamarin.

Hakazalika, Hukumar ta tura jami'anta na ƙananan hukumomi 44 tare da Babban Kwamitin Sa-Ido na Jiha domin gudanar da bincike kan masu yaɗa irin waɗannan saƙonni da hotuna da ake zargi masu tayar da hankali.

Sai dai hukumar ta ce har zuwa yanzu ba a gano waɗanda ke aikata irin wannan aiki ba, amma binciken yana ci gaba.

A cewar sanarwar, Hukumar ta yi la'akari da yarjejeniyar kasuwanci da wasu daga cikin masu wannan sana'a suka ƙulla da masana'antar Kannywood, musamman ta fuskar rarrabawa da dillancin fina-finai.

"Bayan dogon nazari, Hukumar ta yi la'akari da muhimmancin ƙarfafa matasa da tallafa musu ta hanyar samar da ingantattun hanyoyin dogaro da kai, domin bunƙasa tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin Jahar Kano. Saboda haka, Hukumar ta bayyana cewa har zuwa wannan lokaci ba ta soke sana'ar downloading ba a fadin Jahar Kano".

Sai dai ta ce za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai kan duk wanda aka samu yana amfani da wannan sana'a wajen aikata abubuwan da suka saɓawa tarbiyya da koyarwar addinin Musulunci.

A ƙarshe, Hukumar ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da haɗa hannu da sauran hukumomin gwamnati, shugabannin ƙungiyar masu downloading da kuma al'umma baki ɗaya domin kawar da duk wata barna da ka iya shafar wannan sana'a.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ƙofarta a buɗe take ga duk wanda ke da wani rahoto ko sahihan bayanai da suka shafi ayyukanta, domin tabbatar da bin doka da oda a kowane lokaci.

Ready to PlayDala FM88.5 FM