Gwamnatin tarayya ta sanar da rage farashin man fetur a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin rage farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen mai na Kamfanin mai na kasa (NNPC) na tsawon kwanaki 30.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da tattalin aziƙin kasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Oyedele ya ce za a samu rangwame kan farashin fetur a gidajen mai na NNPC na tsawon wata guda, inda za a bai wa masu motocin jigilar fasinjoji fifiko.
Ya ce: “Za a samu rangwame kan fetur a NNPC na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu harkar jigilar jama’a fifiko.”
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta cimma matsaya kan sabon farashin saukar da man fetur (landing cost), wanda za a rika duba shi duk wata.
Ya ce matakan na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage wa ’yan Najeriya nauyin tsadar man fetur, musamman masu zirga-zirgar jama’a da fasinjoji.



