Zargin Kisan kai: Kotu ta aike da matashi Lurwanu Ya'u gidan gyaran hali a Kano.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Kotun majistret mai lamba 27, da ke jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Hauwa Abba, ta aike da wani matashi gidan gyaran hali bisa zargin aikata laifin kisan kai.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, matashin mai suna Lurwanu Ya'u, ana zargin sa ne da laifin kashe wani matashi mai suna Buhari Haladu sakamakon rashin fahimtar da ya shiga tsakaninsu a ƙauyen Kera da ke ƙaramar hukumar Gaya.
Wakilin Dala FM Kano Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa, kotun ta kuma yi umarni ga lauyoyin gwamnati da su fitar da shawara domin ɗaukar mataki na gaba.


