Hisbah ta kama maza da mata 16 bisa zargin su da baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu maza 6, da mata 10, a wani sumame da ta kai na daƙile baɗala cikin dare a unguwar Ɗanbare da yankin Yahaya Gusau.
Mataimakin Babban Kwamandan hukumar a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden Abubakar, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM, a ranar Alhamis 18 ga Yuni, 2026.
Ya ce hukumar ta kamo maza da matan ne a cikin daren ranar Laraba 17 ga Yuni, 2026, a wani sumame da suka kai a Kanem Suites da ke titin Yahaya Gusau, da hanyar zuwa Jami'ar Bayero, da kuma unguwar Ɗanbare da Layin Shisha bayan korafe-korafen da hukumar ta samu kan zargin aikata baɗala a yankunan.
Dr. Mujahideen Aminudden ya kuma ƙara da cewa, duba da cewar hukumar bata taɓa kama matasan ba, a don haka ta ɗauki matakin yi musu wa'azi na musamman tare da miƙa su hannun iyayen su.



