Sojoji sun ceto sauran mutane 4 da aka yi garkuwa da su tare da marigayi Manjo janar Rabe Abubakar

Dakarun sojin Najeriya sun ceto sauran mutane hudu da aka yi garkuwa da su tare da marigayi Janar mai ritaya, Rabe Abubakar, a Jihar Katsina.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ya fitar a ranar Laraba, 17 ga Yuni, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen da aka ceto sun hada da Musa Yakuba mai shekaru 62, da Alhaji Sa’adu Dayi mai shekaru 68, Mukhtar Danja mai shekaru 36 da Salisu Danja mai shekaru 50.
A cewar sanarwar, an ceto su ne yayin da dakarun soji ke ci gaba da gudanar da farmaki domin kamo shugaban ’yan bindiga, Kachalla Muhammadu Fulani, da mabiyansa.
Haka kuma, jami’an lafiya sun bai wa waɗanda aka ceto kulawa bayan sun samu raunuka na harbin bindiga a lokacin da suke hannun masu garkuwa da mutane.
Sanarwar ta ƙara da cewa an riga an ceto matar marigayi Janar Rabe Abubakar, yayin da mutanen da aka ceto suke cikin waɗanda aka gani tare da shi a wani hoto kafin rasuwarsa, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.
Kwamishinan tsaron ya jaddada cewa jami’an tsaro na ci gaba da bibiyar Kachalla Muhammadu Fulani, da sauran masu aikata laifuka, yana mai cewa farmakin zai ci gaba har sai an kamo duk waɗanda ke da hannu a ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane a jihar ta Katsina.



