Mun baza zaratan jami'ai da za su samar da tsaro a yayin bikin Takutaha a Kano - Rundunar KOSSAP

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye ta Anti Illicit Drugs and Phone Snatching Force a Kano, ta ce ta baza zaratan jami'ai da za su shiga lungu da sako domin gudanar da ayyukan tsaro a yayin bikin Takutaha.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake bayyana shirin rundunar kan yadda suka tanadi zaratan ma'aikata na farin kaya da masu sanye da Kaki, da za su shiga lungu da saƙo domin daƙile shirin ɓata garin da ke tada hankalin al'umma.
A yau Talata 1 ga watan Satumban 2026, ne dai za a gudanar da bikin Takutaha, a wani ɓangare na murnar zagayowar ranar sunan Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, wato 19 ga watan Rabi'ul Awwal 1448. Bayan hijira.
Sai dai Nura Sharaɗa, ya gargaɗi dukkanin ɓata garin matasan da suke fakewa a cikin masu gudanar da bikin Takutahar suna tada hankalin al'umma, da kuma satar kayan mutane da su kiyaye su shiga hankalin su kasancewar duk wanda suka kama ba zai ji da daɗi ba.
A cewar sa, "Duk matashin da ya san ba bikin Takutaha zai je ba zai fita ne domin ya tada hankalin jama'a, to ya kiyayi kansa domin ba za mu saurara wa dukkan wanda muka kama ba da aikata wani laifi," in ji shi.
Kwamandan rundunar ta Anti-Phone Snatching Force, wacce akafi sani da KOSSAP, Nura Sharaɗa, ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara jan ƴaƴansu a jiki tare da tsawatar musu kan su guji aikata miyagun ayyuka, domin gujewa yin abinda za su zo suna yin dana sani.
Ya kuma ce jami'an su za su ƙara baza koma wajen faɗaɗa sintiri a sassa daban-daban na jihar Kano, domin yaƙi da faɗan daba, da ƙwacen waya da kuma sha da fillancin kayan maye a faɗin jihar nan, domin ƙara samun zaman lafiya a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.



