Koma Labarai
Labarai

Ƙaunar da nake yi wa Muslunci ce ta sa nake goyon bayan takarar Muslim-Muslim, Sheikh Jingir

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƙaunar da nake yi wa Muslunci ce ta sa nake goyon bayan takarar Muslim-Muslim, Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar malamai ta Ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce ƙaunar da yake yi wa Muslunci ce ta sa yake goyon bayan takarar Muslim-Muslim, ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai ranar Talata a Kano, a Hedikwatar ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa NUJ, reshen jihar Kano, a wani ɓangare na ziyarar aiki da ya kai jihar.

A ranar Asabar 8 ga watan Agustan 2026, ne dai, a wajen walimar auren gata da gwamnatin Kano ta yi wa mutane 3,000, Sheikh Sani Jingir, ya jaddada aniyar sa ta buƙatar takarar Muslim-Muslim, ta shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Sai dai kalaman malamin sun janyo cece-kuce tare da shan martani, inda aka jiyo tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da Hukumar kare hakkin bil'adama, da dai sauran su, sun ƙalubalanci kalaman sa.

Sai dai Sheikh Jingir ya ce, har yanzu yana kan bakar sa ta yin Muslim-Muslim a ƙasar nan, kuma yana kai har ya mutu ba zai daina ba.

Ya ce ƙaunar da yake yi wa Muslunci ce ta sa yake goyon bayan takarar Muslim-Muslim, ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Da aka yi masa tambayar shin yana kan tsarin Muslim-Muslim ne da yawuna Ƙungiyar Izala ko yana yi ne a raɗin kan sa, Sai ya ce yana Muslim-Muslim, ne a iya raɗin kan sa, ba wai matsaya ce ta Ƙungiyar Izala a ƙasar.

Shugaban Majalisar malamai ta Ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya kuma musanta zargin da wasu ke yaɗawa na cewar ya ce ka da a zaɓi Kirista a yayin zaɓen 2027.

A cewar sa, a bayanan da ya yi a baya, babu inda ya ce kada a zaɓi Kirista a zaɓen 2027, da ke tafe, ƙarya ce da wasu ke yaɗawa domin bai faɗi hakan ba.

Sheikh Jingir ya kuma ce, ya buƙaci a yi Muslim-Muslim ne domin ƙara samun haɗin kai da zaman lafiya a sassan Najeriya, kuma ba don Tinubu yake yin Muslim-Muslim ɗin ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM