Ana zargin wani mutum da ɗaukar ma'aikata da sunan Gwamnatin Kano, ta ofishin Shugaban Ma'aikata na bogi.

Wasu masu neman aikin gwamnati a Kano sun yi zargin cewa, an karɓi kuɗaɗensu da sunan samar musu guraben aiki a ma’aikatu daban-daban, inda aka bai wa wasu takardun ɗaukar aiki tare da fara biyansu albashi na watanni biyu kafin biyan ya tsaya.
Ɗaya daga cikin masu korafin, Abdullahi Yahaya Adam, ya ce wani mutum ne mai suna Adamu Aliyu Yahaya, ya sayar musu da takardun ɗaukar aikin (Offer), waɗanda aka ce an buga su ne a Sakatariyar Audu Bako, ya ce daga baya bincikensu ya nuna akwai matsala game da sahihancin takardun.
Abdullahi ya ce, da fari sun kai ƙorafi ga Hukumar Tsaro ta Civil Defence, inda aka kama mutumin tare da tsare shi na kusan makonni uku, kafin daga bisani a sake shi bisa umarnin kotu, inda su ke zargin tun bayan sakinsa ba su sake samun sa ba, kuma ba a mayar musu da kuɗaɗensu ba.
Masu korafin sun kuma ce, an karɓi kuɗaɗe tsakanin naira dubu 450 zuwa dubu 500 daga hannun wasu da sunan guraben aiki a Ma’aikatun lafiya, Ƙananan Hukumomi, Kasuwanci da Kuɗi da kuma KSMB.
A karshe sun roƙi Gwamnan Kano ya sa a gudanar da bincike tare da taimaka musu wajen kwato musu haƙƙoƙinsu.



