Koma Labarai
Labarai

Zaman bola da ƙasƙanci sh ine sakamakon masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi - NDLEA a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Zaman bola da ƙasƙanci sh ine sakamakon masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi - NDLEA a Kano.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA reshen jihar Kano, ta bayyana cewa masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi na fuskantar ƙasƙancin rayuwa har ta kai su ga haukacawa.

Shugaban hukumar a nan Kano Alhaji Ɗahiru Yahaya Lawan ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai a ranar Litinin 6 ga watan Oktoba, 2026.

Ya ce ta'ammali da miyagun ƙwayoyi kan janyo wasu har iayensu suke kashewa.

Ɗahiru Yahaya ya bayyana wasu alamomi da suka haɗar da yawan bacci, da yawan kashe kuɗi da sace-sace, da kuma ƙazanta, da taɓarbarewar tarbiyya da canjin ɗabi'a a matsayin alamomin fara shaye-shaye.

Alhaji Lawan ya kuma shawarci iyaye da su dinga kai ƴaƴansu hukumar domin yin gwaji da shawarwari idan sun ga alamar soma shaye-shaye a wajen ƴaƴansu.

Kwamandan ya yi wannan jawabin ne a dai-dai lokacin da aka gurfanar da wani matashi a kotu bisa zargin yunƙurin dukan mahaifiyarsa sakamakon ya sha wata haramtacciyar ƙwaya.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa, shugaban hukumar ya bayyana gamsuwarsa da matakin da gwamnatin jahar Kano, ta ɗauka a kan batun yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM