Ƙungiyar Matasa Musulmi ta ɗauki nauyin duba marasa lafiya 300, tare da basu magunguna kyauta a Kano.

Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Jihar Kano (KAMYA) ta ɗauki nauyin duba marasa lafiya 300, tare da yi musu gwaje-gwaje da kuma basu magunguna kyauta a yankin Ja'en da ke ƙaramar hukumar Gwale.
Shugaban ƙungiyar ta KAMYA, a Kano, Imam Muntaka Abdulmalik, ne ya ƙaddamar da gangamin duba lafiya da kuma bada magungunan kyauta ga al'umma da ya gudana a Firamaren Ja'en da ke ƙaramar hukumar Gwale.
Imam Muntaƙa ya kuma ƙara da cewa, sun gudanar da duba lafiya da bada magungunan ne haɗin gwiwa da ƙungiyar The Mum’s Care Charity Initiative karkashin jagorancin Hajiya Dr. A’ishatu Joda.
A jawabin bude taron, Imam Muntaka ya bayyana cewa, shirin na daga cikin alkawuran da ya ɗauka a ranar rantsar da shi a matsayin Shugaban KAMYA Karo na Uku, na fadada ayyukan jin ƙai zuwa ƙananan hukumomi daban-daban.
A cewar sa, "A yayin gangamin mun yi wa maza da mata, da yara gwaje-gwajen lafiyar tare da basu magungunan kyauta domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa, duba da halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki," in ji shi.
Shugaban ƙungiyar ta matasa musulmi ta jihar Kano KAMYA, Imam Muntaƙa Abdulmalik, ya kuma yi kira ga masu hali da su ƙara tashi tsaye wajen tallafawa masu ƙaramin ƙarfi domin taimakawa rayuwar su.
Waɗanda aka duba aka basu magungunan kyauta, sun bayyana farin cikin su, inda suka miƙa godiyar su ga ƙungiyoyin biyu bisa yi musu gwaje-gwajen da kuma basu magungunan kyauta.



