A gaggauta ɗaukar mataki dangane da kisan gillar da aka yi wa malamar islamiyya a Kaduna - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta yi Allah wa-dai da kakkausar murya kan mummunan kisan gillar da wasu fusatattun matasa suka yi wa wata malamar makarantar Islamiyya, a mararrabar Jos, da ke jihar Kaduna.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Babban Daraktan Ƙungiyar a Najeriya, Ambasada Ƙaribu Yahaya Lawan Kabara, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, a ranar Litinin 22 ga Yuni, 2026.
A ranar Lahadi 21 ga Yuni, 2026, ne dai matasan suka kashe matar mai suna Ummulkhairi, ta hanyar ƙona ta da wuta, bisa zargin ta da satar yara, al'amarin da ƴan uwa, da mijin ta suka musanta zargin.
A cewar sa, "Mu na jaddada cewa jinin wannan malamar makarantar Islamiyya ba zai tafi a banza ba, domin za mu yi duk mai yiyuwa domin ganin an bi wa iyalan ta hakƙin jinin ta, in ji Ƙaribu.”
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin jihar Kaduna, da rundunar ƴan sandan jihar, da dukkan masu ruwa da tsaki, da a gaggauta ɗaukar matakin bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa baturen ƴan sandan yankin da lamarin ya faru, bisa zargin da ake yi masa, da jami'an sa na taka rawa har matasan suka kashe matar.
Ambasada Ƙaribu Kabara, ya kuma ce dole ne a tabbatar da gaskiya tare da hukunta duk wanda bincike ya tabbatar yana da hannu a wannan kidan gillar, ba tare da nuna son kai ko kariya ga kowa ba.
Haka kuma, Ƙungiyar ta Global Community for Human Rights Network a Najeriya, ta baiwa hukumomin da abin ya shafa wa'adin kwanaki (7) da su fito da sahihan sakamakon bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace bisa doron doka, ko su garzaya gaba.
A cewar Babban Daraktan ƙungiyar a Najeriya, idan har ba a yi hakan ba, za su yi amfani da dukkanin hanyoyin doka da ku din tsarin mulki ta tanada, domin neman adalci ga marigayiyar da iyalan ta.
Ƙaribu Kabara, ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna, da ta tallafa wa mijin marigayiyar da ƴaƴan ta, tare da ba su diyya, da kulawar da ta dace domin rage musu wani radaɗin babban rashin da suka yi.



