El-Rufa'i ya maka ICPC a kotu yana neman diyyar Naira biliyan 10 kan hana iyalansa ganinsa
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya shigar da ƙarar Naira biliyan 10 a kan hukumar ICPC, bisa zargin hana matarsa Aichatou Asabe da ɗansa Abba ganinsa yayin da yake tsare.
A ƙarar da ya shigar, Mallam Nasir El-Rufa'i ya kuma haɗa Shugaban ICPC da Antoni-Janar na Tarayya, ya ce hana iyalansa ganinsa ya tauye masa haƙƙin ɗan Adam da na rayuwar iyali da kundin tsarin mulki ya ba shi.
Kafar DCL ta ruwaito cewa, El-Rufa'i ya nemi Babbar Kotun Tarayya da ta umarci ICPC ta ba iyalinsa da lauyoyinsa damar ganinsa yadda ya kamata, a tsawon lokacin da yake tsare.
Ya kuma yi zargin cewa an hana matarsa kai masa abinci, da magunguna da kuma sauran abubuwan da yake buƙata.



