Shugaba Tinubu ya umurci EFCC ta buɗe asusun bankin gwamnatin jihar Osun da ta kulle

Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya umurci Hukumar EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin janye umarnin da ta samu na dakatar da asusun gwamnatin jihar Osun.
Wannan na cikin wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta ya fitar a ranar Alhamis 6 ga Agustan 2026.
Tinubu ya ce ko da yake bai saba tsoma baki cikin ayyukan hukumomin yaƙi da cin hanci ba, ya damu da lokacin da aka bijiro da matakin, kasancewar jihar Osun na gab da gudanar da zaɓen gwamna.
Shugaban ya ce bai san da matakin EFCC tun da farko ba, amma ya yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗauki wani mataki da zai iya haifar da zargin cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin yin tasiri kan zaɓen ba.
Saboda haka ne ma ya umurci EFCC da ta janye umarnin kotun, tare da dakatar da duk wani mataki da ta ɗauka kan gwamnatin jihar Osun domin kare mutuncin tsarin dimokuradiyya, kamar yadda kafar DCL Hausa ta ruwaito.



