Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta umarci a karɓe wayoyin Jarumar Kannywood Rashida Mai Sa'a tare da hana ta yin rubutu a soshiyal midiya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta umarci a karɓe wayoyin Jarumar Kannywood Rashida Mai Sa'a tare da hana ta yin rubutu a soshiyal midiya

Kotun majistret mai lamba 7 ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Halima Wali, ta fara sauraren wata ƙara wadda yansanda suka gurfanar da Rashida Adamu Abdullahi wadda aka fi sani da Rashida mai Sa'a.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar ana zargin Rashida da laifin ɓata suna da cin mutunci da hana zaman lafiya.

Sai dai yayin da aka karanta mata ƙunshin tuhumar da ake yi mata ta musanta a gaban kotun.

Yayin zaman kotun na ranar Litinin 11 ga Mayu, 2026, Mai ƙara Ruƙayya Dawayya ta bayyana cewar Rashida mai Sa'a ta hau kafar sadarwa ta zamani ta ci mutuncin ta.

Mai shari'a Halima Wali ta sanya Rashida a hannun beli bisa sharaɗin cewa sai ta gabatar da ɗan majalisar jaha, da kuma ɗan uwanta wanda ya mallaki gida na naira miliyan ɗari uku, idan ta tsere masu karnar belin za su ajiye Naira miliyan goma.

Sannan kotun ta yi umarnin a karɓe wayoyinta, kuma kar ta kuma wallafa wani abu a shafukanta na kafafen sadarwa har sai an kammala shariʼar.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa kotun ta sanya ranar 20 ga watan Mayun da muke ciki domin ci gaba da shariʼar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM