Koma Labarai
Labarai

Kamfanin Ɗangote ya rage farashin man fetur ɗinsa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kamfanin Ɗangote ya rage farashin man fetur ɗinsa

Rahotanni sun bayyana cewa matatar Mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur PMS da Naira 50 kan kowace lita, karo na huɗu cikin wata guda.

Matatar ta ce ya rage farashin fetur da jimillar Naira 200 kan kowace lita tun daga ranar 30 ga watan Mayun 2026.

Matatar ta kara da cewa farashin daga kamfanin ya sauka zuwa Naira 1,075 kan kowace lita daya, kamar yadda kafar DCL Hausa ta ruwaito.

Ready to PlayDala FM88.5 FM