Koma Labarai
Tsaro

Rundunar Civil Defense a Kano, ta cafke mutane biyu ɗauke da wata saniya ta sata a ƙaramar hukumar Ƙiru

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar Civil Defense a Kano, ta cafke mutane biyu ɗauke da wata saniya ta sata a ƙaramar hukumar Ƙiru

Rundunar tsaro ta Civil Defense a nan Kano ta kama wasu mutane biyu da take zargin barayin Shanu ne dauke da wata Saniya ta sata a karamar hukumar Kiru.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar tsaron ta Civil Defense a nan Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana wa Dala FM kama mutanen biyu a ranar Laraba 26 ga watan Agusta, 2026.

Ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da Jami'in rundunar suke a bakin aiki a shingen bincike a Tudunwada Rahama Rawun.

SC Ibrahim Abdullahi ya kuma ƙara da cewa, jami'an nasu sun kama waɗanda ake zargin ne da tsakar dare ɗauke da Saniyar da ake zargin ta sata ce.

Rahotanni dai sun kuma bayyana cewa, tuni Jami'an rundunar suka cigaba da gudanarda bincike akan faruwar lamarin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM