Koma Labarai
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Wasila Isma'il ta rasu

Hassan Mamuda Ya'u 17 views
Tsohuwar jarumar Kannywood, Wasila Isma'il ta rasu

Rahotanni sun bayyana cewa tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Isma'il ta rasu, sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

Shugaban hukumar tace fina-finai da Ɗab'i ta jihar Kano, Abba Al-Mustapha ne ya sanar da rasuwar marigayiyar.

Wasila Isma'il dai guda ce daga cikin tsofaffin jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Shima Aminin tsohon mijinta Aliyu Abdullahi Gora, an gano yadda ya wallafa sanarwar rasuwarta a shafinsa na Facebook, kamar yadda kafar DCL ta ruwaito.

Har ila yau, Tashar Dala FM Kano, ta gano yadda itama fitacciyar marubuciya, kuma mai rajin tallafa wa mabuƙata, Fauziyya D Sulaiman, ta wallafa rasuwar tsohuwar jarumar a shafin ta na Facebook, tana addu'ar Allah ya jiƙan ta.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM