Guda daga cikin ma'aikatan Freedom Radio Kano, Injiniya Kamal Muhammad Jamil ya rasu.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Hukumar gudanarwa ta Freedom Radio na sanar da rasuwar ma’aikacinta, Injiniya Kamalu Muhammad Jamilu, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a safiyar yau Talata, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Za’a gudanar da jana’izarsa a gidansu da ke Unguwar Hotoro, kan Titin Kanal Daudu, da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar yau.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.
Allah Ya ba iyalansa, ’yan uwa da abokan arziki haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.
Tuni dai al'umma ke ci gaba da bayyana alhinin su dangane da rasuwar Marigayin.



