Koma Labarai
Labarai

Mun haura shekaru 44 a garin Gwamma da ke Bunkure, amma rana ɗaya wani mutum ya ce mu tashi an sayar masa da burtalan yankin mu - Fulani a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mun haura shekaru 44 a garin Gwamma da ke Bunkure, amma rana ɗaya wani mutum ya ce mu tashi an sayar masa da burtalan yankin mu - Fulani a Kano

Fulani makiyaya da ke zaune a Garin Gwamma a ƙaramar hukumar Bunkure, sun nemi ɗaukin gwamnatin jihar Kano, kan yadda suka ce wani mutum ya basu umarnin su tashi daga gidajen su, bayan da ya ce musu an sayar masa da burtalan yankin.

Fulanin sun bayyana cewa, aƙalla sun haura shekaru 44 suna zaune a garin na Gwamma tun kafuwar sa, ba tare da fuskantar wata matsala daga ɓangaren gwamnati ko kuma abokan zaman su Manoma ko jami'an tsaro ba.

Sun ce sai gashi rana ɗaya tsaya wani mutum mai suna Alhaji Kabiru, ya zo ya umarce su da cewar su tashi daga yankin, inda ya sanar musu cewa wai an sayar masa da burtalan da rigar su ke ciki amma ba tare da ya nuna musu wata shaida da za bada tabbacin an sayar masa da burtalan ba.

Fulanin sun ce, umarnin da mutumin ya basu na cewar su tashi daga gidajen nasu, tare da kwashe dukkanin Shanun su, da sauran kayayyakin su, ya matuƙar tayar musu da hankali, lamarin da ya sa mafi yawan su ba ma sa iya yin bacci a yanzu saboda rashin kwanciyar hankali.

Alhaji Shehu Bunkure, Bafulatani ne mai shakaru 80, wanda shi ne ya fara tarewa a garin na Gwamma da ke ƙaramar hukumar Bunkure, ya ce ya yi mamaki kan yadda Alhaji Kabiru, ya zo rana ɗaya tsaka ya ce su tashi daga gidajen su da ke burtalan, bayan da ya ce an sayar masa.

Ya kuma yi kira ga gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da dukkanin waɗanda lamarin ya shafa da su kai musu ɗaukin da ya dace, domin daƙile manufar mutumin da ke iƙirarin cewar an sayar masa da makiyayar rigar fukanin, tunda dai gwamnati ta ce burtalan ba na sayarwa ba ne.

Muhammadu Lawan Dunkura Sabuwar Unguwa, shi ne shugaban ƙungiyar Fulani ta Gan Allah, ta jihar Kano, reshen ƙaramar hukumar Bunkure, ya shaidawa Dala FM Kano cewa, tun bayan da Fulanin suka miƙa musu koken su ne suka tashi tsaye zuwa wajen mahukunta domin ganin an ɗauki matakin da ya dace amma kawo yanzu shiru.

A cewar sa, shima a baya, sai da mutumin da suke zargi ya yi sanadiyyar zama a gidan yari inda ya yi kwanaki uku a ciki, sakamakon kai shi kotu da ya yi dukka a kan sun ƙi tashi daga makiyayar su da ke Burtalan gwamnati.

Kan batu wannan batu ne muka tuntuɓi wanda ake zargi da cewar an sayar masa da burtalan a garin Gwamma, da ma wasu yankuna na ƙaramar hukumar Bunkure, mai suna Alhaji Kabiru, ta wayar salula, inda ya musanta zargin tashin Fulanin, har ma ya ce an sayar masa da wajen ne kusan shekaru 4 da suka gabata.

Ko da muka tambaye shi a wajen wanda ya sayi wajen sai ya ce mu bashi lokaci zai yi mana ƙarin bayani akai, amma kawo lokacin da muke kammala haɗa wannan labarin bai yi mana ƙarin bayanin ba, duk da kiran sa da muka kara yi.

Kasancewar an yi taron masu ruwa da tsaki kan lamarin a garin Gwamma a ranar Litinin 10 ga watan Agustan 2026, inda Shugaban ƙaramar hukumar Bunkure, Muhammad Aliyu Bashir Barkum, ya ce, babu wanda zai tashi Fulanin.

A cewar sa, "Yanzu haka Gwamnati tana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wanda yake ikirarin an sayar masa da wajen tare da ɗaukar mataki na gaba a kan duk wanda aka samu da hannu a kan lamarin," in ji shi.

Itama da take nata jawabin, mai taimakawa gwamnan Kano a kan harkokin Fulani, Ruƙayya Umar Gadanƙaya, ta ce gwamnati za ta yi abinda ya dace a kan lamarin.

A yayin taron masu ruwa da tsaki gami da jin ra'ayoyin ƙorafe-ƙorafen fulanin yankin, al'umma da dama ne suka halarta ciki har da wakilci daga Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, da jami'an gwamnati, da jami'an tsaro, da shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah, (MAGBAN) da dai sauransu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM