Koma Labarai
Labarai

Hajjin 2026: An sanya ranar fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hajjin 2026: An sanya ranar fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya

Hukumar kula da aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da cewa, za a fara jigilar maniyyata daga Najeriya zuwa Kasa Mai Tsarki, domin aikin Hajjin bana na shekarar 2026 a ranar 3 ga watan Mayun 2026.

Hukumar ta ce tafiyar farko za ta tashi ne daga sabon filin jirgin sama na Kasa-da-Kasa na Gateway da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, inda kamfanin jirgin FlyNas zai kwashe maniyyatan jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan shi ne karon farko da maniyyatan Jihar Ogun za su tashi kai-tsaye daga jiharsu tun bayan gina filin jirgin saman a jihar.

Baya ga Jihar Ogun, sauran jiragen da za su tashi a wannan rana sun haɗa da Kamfanonin Umza da Max Air, da za su kwashe maniyyatan jihohin Kogi da Nasarawa daga Abuja, sai Kamfanin Air Peace da zai kwashe maniyyatan Jihar Oyo daga Legas.

Kazalika daga Birnin Kebbi, wani jirgin na FlyNas zai tashi da maniyyatan Jihar Kebbi.

Yayin da ake shirin fara jigilar, tuni jami’an NAHCON da suka haɗar da tawagar likitoci suka sauka a ƙasar Saudi Arabiya a yau Talata, 28 ga watan Afrilu, domin yin shirye-shiryen tarɓar maniyyatan Najeriya.

Hukumar NAHCON, ta fitar da wasu muhimman shawarwari kamar haka:

Tsarin Shiyya (Zones): Kowanne kamfanin jirgi zai kwashe maniyyatan shiyya ɗaya ne a lokaci guda, da zarar an gama da shiyya aka koma gaba, jirgi ba zai sake dawowa wannan shiyyar ba. Duk maniyyacin da ya rasa jirginsa, zai dauki nauyin bin jirgin zuwa inda ya dosa ko kuma ya jira har sai an sake tsara tafiyarsa.

Tsarin Rukunin Mutum 45: Dole ne kowane maniyyaci ya yi tafiya a cikin rukuninsa na mutum 45.

Katin Nusuk na maniyyata suna nan a shirye suna jiran isowarsu Saudi Arabiya.

Ana shawartar maniyyata su san sauran mambobin rukuninsu, sannan su tanadi lambobin wayar shugabannin rukuninsu da na jami’an jihohinsu.

Shugaban hukumar NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya ba wa maniyyatan kasar tabbacin cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da an gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin nasara da sauki.

A halin yanzu dai, maniyyata na ci gaba da shirin karshe na bankwana da iyalansu gabanin fara fita zuwa filayen jirgi a mako mai zuwa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM