Koma Labarai
Labarai

Ana ci gaba da alhinin rasuwar fitaccen mai sharhi kan harkokin jama’a Comrd. Bello Sharada a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ana ci gaba da alhinin rasuwar fitaccen mai sharhi kan harkokin jama’a Comrd. Bello Sharada a Kano.

Fitaccen mai sharshi kan harkokin jama’a, kuma ƙwararren ɗan jarida, kazalika marubuci a Kano, Kwamared Bello Muhammad Sharada, ya rasu yana da shekaru 56.

Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar 29 ga watan Agusta, 2026, a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Bello Sharaɗa, ya shahara wajen sharshi da nazari kan al’amuran siyasa da sauran batutuwan da suka shafi Najeriya, musamman ta kafafen sada zumunta, ciki har da shafin Facebook.

Kafin rasuwar marigayin ya kasance mai goyon bayan siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Kafar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a tsawon rayuwarsa, Marigayin ya taka rawa wajen bunƙasa muhawarar jama’a ta hanyar rubuce-rubuce da sharhinsa kan sauye-sauyen siyasa da sauran al’amuran ƙasa.

Bayan rasuwarsa, abokai, abokan aiki da sauran al’umma sun bayyana alhininsu, inda suka bayyana marigayin a matsayin mutum mai kishin rubutu da bayar da gudunmawa wajen wayar da kan jama’a.

An shirya gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Lahadi a Sharada Fegi, cikin ƙaramar hukumar Kano Municipal, bisa tsarin addinin Musulunci.

Marigayin ya rasu ya bar iyalai da sauran ’yan uwa da abokan arzuka.

Ready to PlayDala FM88.5 FM