Koma Labarai
Labarai

Mutuwar mutane 37: Gwamnatin jihar Neja ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a Minna

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mutuwar mutane 37: Gwamnatin jihar Neja ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a Minna

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya sanya dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24 a garin Minna, babban birnin jihar, sakamakon tashin hankalin da ya ɓarke a wasu sassan birnin.

Dokar ta fara aiki nan take bayan kammala sallar Juma’a, kuma za ta ci gaba da aiki har sai gwamnati ta fitar da wata sanarwa ta daban.

A cikin sanarwa da gwamnatin ta fitar, an umarci mazauna Minna da su zauna a gidajensu tare da guje wa duk wata zirga-zirga da ba ta da muhimmanci a lokacin dokar.

Haka kuma, gwamnatin jihar ta umarci jami’an tsaro da su tabbatar da cikakken aiwatar da dokar, tare da daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Matakin na gwamnan ya biyo bayan zanga-zanga da rikicin da ya faru a Minna ranar Alhamis, wanda ake danganta shi da mutuwar wasu mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adanan ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen sun rasu ne a lokacin da suke tsare a hannun Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta ƙasa (NSCDC) a Minna, da ke jihar Neja.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga mazauna birnin da su kwantar da hankalinsu, su zauna a gidajensu tare da bin umarnin jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM