Koma Labarai
Masarauta

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, zai gudanar da Hawan Sallar Ghani, a jihar.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, zai gudanar da Hawan Sallar Ghani, a jihar.

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, zai gudanar da Hawan Sallar Ghani, a jihar.

Shugaban tawagar ƴan Soshiyal Midiya na Masarautar Kano, Yakubu Ibrahim Dogarai, wanda akafi sani da Abba Lafazi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook, ranar Juma'a 28 ga Agusta, 2026.

Ya kuma ce sarkin zai gudanar da Hawan Sallar Ghani, ne domin taya ƴan uwa murnar zagayowar watan da aka haifi Manzon Tsira Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, a cewar sanarwar za a gudanar da Hawan ne a yammacin ranakun Asabar 29, da Lahadi 30 ga watan Agusta, 2026, a birnin Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM