Ka da ku biya wa mutane aikin Hajji da Umrah da kuɗin sata - Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya gargadi ’yan siyasa da masu rike da muƙaman gwamnati da su guji daukar nauyin mutane zuwa Makka ko Kudus da kudaden da aka sace daga dukiyar al’umma.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Sultan ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Laraba yayin buɗe taron masu ruwa da tsaki na majalisar addinai ta Najeriya (NIREC) a Abuja.
Sarkin ya ce bai kamata a yi amfani da kuɗaɗen rashawa wajen gudanar da ayyukan ibada ba.
Ya kuma yi kira ga shugabannin addinai da su haɗa kai da hukumomin yaƙi da cin hanci wajen daƙile rashawa.
Ya kuma bukaci EFCC ta hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen cin hanci ba tare da la’akari da addininsa ko matsayinsa na siyasa ba.
Sarkin ya kuma gargadi malamai da su guji kalaman da za su haddasa rarrabuwar kawuna, musamman a lokacin zabuka, inda ya bukace su da su rika yi wa shugabannin kasa addu’a.
A nasa bangaren, Shugaban kwamitin shawara kan yaki da cin hanci tsakanin Addinai, Farfesa Adedibu Ojerinde, ya ce an samar da littattafan yaki da rashawa domin taimakawa malamai wajen isar da sakonnin yaki da cin hanci a masallatai da coci-coci a ƙasar.



