Koma Labarai
Tsaro

Gwamnatin Kano na nuna mana halin ko in kula kan matsalar tsaron yankin mu - Mazauna Ɗorayi

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano na nuna mana halin ko in kula kan matsalar tsaron yankin mu - Mazauna Ɗorayi

Al'ummar unguwannin Ɗorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano, sun bayyana ɓacin ransu dangane da yadda gwamnatin jihar Kano, ke nuna musu halin ko in-kula game da matsalar tsaron ke damun su.

Shugaban Gamayyar Kwamitocin tsaro na unguwannin Ɗorayi aƙalla guda 28, da ci gaban yankin, Mallam Abdullahi Idris Ɗan Fodiyo ne ya buƙaci hakan a yayin wani taron manema labarai da suka gudanar cikin yankin, a ranar Juma'a 26 ga Yuni, 2026.

Mallam Abdullahi Ɗanfodiyo ya ce, sun kira taron manema labaran ne domin nuna takaicin su dangane da yadda ake nuna halin ko in kula wajen samar da ci gaban yankin, da ma magance musu matsalar tsaron da take damunsu, duk da irin ƙoƙarin da suke yi wajen bada gudunmawar su ta ko wanne ɓangare.

A cewar sa, "A kwanakin baya sai da muka ce mun daina aikin yaƙi da tsaron bisa yadda gwamnatin Kano, da masu ruwa da tsaki, da kuma mazauna yankin Ɗorayi, suka gaza gode mana kan ƙoƙarin da muke yi, in ji Ɗanfodiyo.”

Sai dai Da fodiyo ya ce, daga bisani ne aka rinƙa roƙon su ka su dawo da aikin samar da tsaro a yankunan na Ɗorayi, hakan ya sa suka dawo, amma dai suna ƙara kira ga gwamnatin jihar Kano, da ta shigo cikin lamarin domin magance matsalolin tsaron.

Da yake nasa jawabin, shugaba Gamayyar Matasan Kano, Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD), ya ce sun rubuta aƙalla takardu sama da guda goma domin buƙatar ganin Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, don su sanar da shi hanyar da za a bi wajen kawar da faɗan daba, tare da wanzar da zaman lafiya a Ɗorayi, amma zuwa yanzu gwamnatin ta gaza amsa buƙatar su.

Muhammad Tijjani MTD, ya kuma yi kira ga gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya ba su dama su gana da shi domin sauraren matsalolin su a kan abinda ya shafi yankin Ɗorayi da kewaye, ta yadda za a magance su, amma ba wakili suke so a haɗa su da shi ba.

A nasa ɓangaren, Babban Daraktan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Awareness for Human Rights and Charity Foundation a Najeriya, Kwamared Auwal Usman Awareness, ya ce akwai ban mamaki ace waɗanda suke ƙokarin ganin an magance faɗan daba, da saura matsalar tsaro a yankin su da ma Kano baki ɗaya, amma gwamnatin jihar ta gaza kai musu ɗauki.

Shima da yake jawabi, guda daga cikin ƴan kwamitin tsaro a Ɗorayi, Sabo Lifidi, ya ce aƙalla kusan shekaru uku ke nan da fara samun faɗan daba a yankin Ɗorayi, kuma akwai sama da matasa dubu biyu da ke ƙoƙarin shawo kan matsalar a yankin, amma gwamnatin Kano ta gaza taimakon su.

A cewar sa "Kwanakin baya gwamnatin Kano ta sa mun miƙa mata sunayen matasan da za a taimaka a yankin mu bisa ƙokarin da suke yi wajen samar da tsaro a Kano, amma har yanzu ba a fara biyan su ba, indai da gaske ake a dawo da batun, in ji Sabo.”

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Ɗumbin al'ummar yankin Ɗorayi da kewaye ne dai suka fito yayin taron manema labaran da ya gudana yau a Ɗorayi, domin nuna damuwar su ga gwamnatin jihar Kano kan matsalar tsaron da suke fuskanta da ma sauran matsaloli, domin ganin an kawo musu ɗauki tare da cire yaudara a cikin lamarin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM