Za a daɗe ba a cike giɓin Marigayi Hamza Usman Darma ba - Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, ta bayyana alhinin ta dangane da rasuwar dattijo Alhaji Hamza Usman Darma, tana mai cewa an yi babban dangane da rasuwar sa.
Shugaban Gamayyar Matasan, kuma shugaban gamayyar ƙungiyoyin matasa da ke rajin hana faɗan daba da shaye-shaye da kuma ƙwacen waya a nan Kano, Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM a Juma'ar nan, biyo bayan rasuwar Marigayin.
An dai yi jana'izar marigayin mai shekaru 67 a yammacin ranar Juma'a 21 ga watan Agusta, 2026, a jihar Kano.
Muhammad Tijjani MTD ya ce rasuwar Marigayi Hamza Usman Darma babban rashin ne a tsakanin al'umma, bisa irin gudunmawar da yake baiwa jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya, kafin rasuwar sa, yana mai cewa za a daɗe ba a cike giɓin sa ba.
A cewar sa, "Da muka fara yaƙi da fadan daba, da shaye-shayen kayan maye, da kuma ƙwacen waya, marigayin muka fara kai wa ziyara, ya kuma bamu shawarwari da nuna damuwar sa a kan lamarin tare da bada gudunmawar sa domin yaƙi da matsalar," in ji MTD.
Ya kuma yi addu'ar Allah ya jiƙan Marigayi Hamza Usman Darma da gafara, da sauran al'ummar Musulmi.



