Koma Labarai
Tsaro

Kafa ‘Yan Sandan Jihohi muhimmin mataki ne na Shugaba Tinubu wajen magance matsalar tsaro a Najeriya – Sanata Barau

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kafa ‘Yan Sandan Jihohi muhimmin mataki ne na Shugaba Tinubu wajen magance matsalar tsaro a Najeriya – Sanata Barau

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin Maliya, ya ce kudirin kafa ‘Yan Sandan Jihohi da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta, wata babbar dabara ce, kuma muhimmin mataki da zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙasar.

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa ta tsawon sa’o’i biyu a shirin Hannu Da Yawa na Radio Nigeria Kaduna, inda ya amsa tambayoyi daga masu sauraro daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.

A cewar sa, "An yi dogon nazari da tattaunawa kan ƙudirin kafin Majalisar Dattawa ta amince da shi, ciki har da sauraron ra’ayoyin jama’a da aka gudanar a shiyyoyi shida na ƙasar nan da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT)," in ji Barau.

Sanata Barau ya kuma ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta fahimci cewa duk da yadda jama’a da dama ke goyon bayan kafa ‘Yan Sandan Jihohi, akwai fargabar yiwuwar amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba. Saboda haka ne aka tanadi matakan kariya domin hana cin zarafi ko amfani da rundunar wajen cimma muradun siyasa ko na ƙabilanci.

Ya bayyana cewa kudirin ya samo asali ne daga haɗin gwiwar Fadar Shugaban Ƙasa, Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, tsofaffin jami’an ‘yan sanda, masana harkokin tsaro, gwamnoni, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce manufar kafa ‘Yan Sandan Jihohi ba wai maye gurbin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ba ce, sai dai ƙara wa tsarin tsaro ƙarfi ta hanyar samar da jami’an da aka ɗauka daga al’ummomin da za su yi aiki a cikinsu.

“Jami’an da aka ɗauka daga yankunansu sun fi sanin mutane, yanayin wurin da ma masu aikata laifuka. Hakan zai taimaka sosai wajen yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka,” in ji shi.

Da yake amsa tambayar Zubairu Mohammed, wani manomi daga Ƙaramar Hukumar Kankiya ta Jihar Katsina, Sanata Barau ya ce jihohin Arewa na daga cikin waɗanda za su fi cin gajiyar wannan tsari saboda yawan matsalolin tsaro da suke fuskanta.

Ya kuma tabbatar da cewa an tanadi matakan doka da za su hana duk wani gwamna ko wata hukuma amfani da ‘Yan Sandan Jihohi wajen tauye haƙƙin jama’a.

Sanata Barau ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kuma Majalisun Dokokin Jihohi su mara wa kudirin baya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen gina tsarin tsaro da ya fi kusanci da al’umma tare da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM