Koma Labarai
Labarai

Tsoro ne ke hana ƴan Arewa neman haƙƙoƙin su kuma hakan ya sa ake ci gaba da zaluntar su - Sadiq Sani Sadiq

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Tsoro ne ke hana ƴan Arewa neman haƙƙoƙin su kuma hakan ya sa ake ci gaba da zaluntar su - Sadiq Sani Sadiq

Fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya ce tsoron da al'ummar Arewacin Najeriya ke yi wa shugabanninsu na daga cikin abubuwan da ke hana su fitowa su nemi haƙƙoƙinsu, lamarin da ke bai wa wasu shugabanni damar ci gaba da zalunci.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Sadiq Sani Sadiq ya bayyana hakan ne a yayin hirar sa da Freedom Radio Kaduna, a cikin shirin Zauren Kannywood, na tashar.

A cewar jarumin mutane da dama na tsoron a kama su, a tsare su ko kuma su fuskanci wasu matsaloli idan suka shiga zanga-zangar neman haƙƙoƙinsu.

Ya ci gaba da cewa, manufar su ita ce su taimaka wajen cire wannan tsoro daga zukatan jama'a domin su fahimci haƙƙoƙinsu da kuma yadda za su neme su ta hanyar lumana da doka ta tanada.

Sadiq Sani Sadiq ya jaddada cewa, wayar da kan jama'a da ƙarfafa musu gwiwa na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da cewa, al'umma na taka rawar gani wajen tafiyar da harkokin dimokuraɗiyya da kuma kare muradunsu.

Sadiq ya yi kira ga jama'a da su fahimci haƙƙoƙinsu na ɗan ƙasa tare da amfani da hanyoyin lumana da doka ta amince da su wajen bayyana ra'ayoyinsu da buƙatunsu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM