Koma Labarai
Labarai

Majalisar Dokokin Kano ta fara nazari kan ƙudirin kafa ƴan sandan Jihar.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisar Dokokin Kano ta fara nazari kan ƙudirin kafa ƴan sandan Jihar.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi Kudirin kafa ’Yan Sandan Jiha, inda ta fara nazarinsa domin duba yadda za a aiwatar da shi.

Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar a ranar Juma'a 2 ga watan Oktoba, 2026.

Shugaban Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya ce an raba kwafin ƙudirin ga dukkan ’yan majalisar domin nazari tare da bayar da shawarwarin gyara idan akwai buƙatar hakan.

Sanarwar ta kuma ce majalisar ta ce an riga an karanta ƙudirin a zaman majalisar, kuma ana sa ran za a gabatar da shi karatu na biyu a ranar 12 ga Oktoba, domin ci gaba da tattaunawa a kai.

Wakilinmu Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, Falgore ya kuma ce Kano na da cikakken shiri na tunkarar matsalolin tsaro, inda yace dokar za ta taimaka wajen ƙarfafa tsarin tsaron jihar.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM