Mun fitar da miliyoyin ƴan Najeriya daga ƙangin talauci daga hawa mulkin mu - Shugaba Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ce a shirye-shiryen tallafin rayuwa da gwamnatinsa ta ba wa ’yan kasar, sun fitar da miliyoyin iyalai daga cikin ƙangin talauci.
Tinubu, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilta a taron bikin Ranar Ma’aikata ta 2026, ya ce gidaje miliyan 15 da ke cikin mawuyacin hali, sun samu tallafin kudi da gwamnatinsa take bayarwa, inda kimanin mutane miliyan 7.5 aka ce sun fita daga kangin talauci.
Jawabin Shugaban Ƙasa a wurin taron da aka gudanar a Dandalin Eagles Square da ke Abuja a ranar Juma’a, ya ce muhimman ayyukan gine-gine da gwamnatin ke yi sun samar da ayyukan yi ga fiye da mutum 600,000 a fadin kasar nan.
Ayyukan a cewar sa sun haɗa da hanyar Legas zuwa Kalaba, da Bututun Iskar Gas na Ajaokuta-Kaduna zuwa Kano.
Kafar Aminiya ta ruwaito cewa, dangane da jin daɗin ma’aikata, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, ta biya bashin fansho da kuma dawo da biyan gratuity tun daga Janairu 2026.
A cewar sa, "Sama da ma’aikata 800,000 daga sashen da ba na hukuma ba, sun shiga shirin micro pension, yayin da ƙananan masana’antu ke amfana da tallafin Naira biliyan 200 na Kananan da Matsakaitan Masana’antu," in ji shi.
A bangaren noma, Tinubu ya ce gwamnati na ci gaba da ƙoƙari wajen inganta noman zamani, noman damina da kuma kare manoma ta hanyar tura jami’an tsaron gonaki na Agro-Rangers 10,000 a jihohi 19.
Ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago, ciki har da NLC da TUC, da su fifita tattaunawa fiye da yajin aiki, yana mai jaddada cewa “yajin aiki ya zama mafita ta ƙarshe, ba ta farko ba.”



