Koma Labarai
Labarai

Shugaba Tinubu ya amince da Kashe Dala Biliyan 3 don gina layin Jirgin Kasa a Kano-Kaduna da Legas

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Shugaba Tinubu ya amince da Kashe Dala Biliyan 3 don gina layin Jirgin Kasa a Kano-Kaduna da Legas

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu, ta amince da bayar da kwangilar gina manyan ayyukan layin dogo guda uku a biranen Kano da Kaduna da kuma Legas, domin bunƙasa tattalin arziƙi da sauƙaƙa zirga-zirga.

Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele ne ya sanar da hakan ga manema labarai a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) da aka gudanar ranar Alhamis 30 ga Afrilu, 2026.

Ministan ya bayyana cewa an zaɓo waɗannan biranen ne saboda matsayinsu na cibiyoyin kasuwanci da suka dogara da kansu, inda ya ce zuba jari a cikinsu zai haifar da sakamako mai kyau ga rayuwar talakawa.

Ayyukan da aka amince da su sun haɗa da:

Birnin Kano: Za a gina layin jirgin kasa na cikin gari (Kano Metro City Rail) wanda zai rinƙa ɗaukar mutane zuwa sassan birnin.

Birnin Kaduna: Za a samar da tsarin jirgin kasa na "Light Rail" (wanda Gwamna Uba Sani ya nuna godiyarsa a kai a safiyar yau).

Birnin Legas: Za a fara aikin layin jirgin kasa na "Green Line" (Phase 1A).

Oyedele ya bayyana cewa waɗannan ayyuka guda uku za su ci kimanin dala biliyan 2.99 (kusan Naira tiriliyan hudu da rabi).

Ya kara da cewa za a samar da kudaden ne ta hanyar kamfanin hannun jari na Ma'aikatar Kudin Kasa (MOFI), tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin bayar da tallafi na musamman.

A cewar sa, "Mun sani cewa babu ci gaba ba tare da ingantattun hanyoyi da sufuri ba, waɗannan ayyukan an tsara su ne don bunƙasa kasuwanci, da sauƙaƙa wa ma’aikata da ɗalibai zirga-zirga, da kuma kyautata rayuwar jama’a a waɗannan manyan biranen," in ji Ministan.

Kafar Dala FM Kano ta ruwaito cewa wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na shirin Shugaba Tinubu na tabbatar da cewa an farfado da bangaren sufuri, domin rage tsadar rayuwa da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a fadin kasar nan.

Masana tattalin arziki na ganin cewa idan aka kammala wadannan ayyukan, birnin Kano da Kaduna za su zama manyan cibiyoyin sufuri a Arewacin Najeriya, wanda hakan zai rage cinkoson ababen hawa da kuma saukaka jigilar kayan amfanin gona.

Ready to PlayDala FM88.5 FM