Koma Labarai
Labarai

Mamallaka filin M ber head da ke Fagge a Kano sun zargi Mallam Ƙalarawi da yunƙurin ƙwace musu fili

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mamallaka filin M ber head da ke Fagge a Kano sun zargi Mallam Ƙalarawi da yunƙurin ƙwace musu fili

Mutanen da ke da mallakar filin M ber head da ke unguwar Fagge daura da kasuwar kwari a Kano, sun koka kan yadda suka ce ɗaya daga cikin malamai a unguwar wato Malam Tijjani Bala Ƙararawi na kokarin kwace musu shi.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin ɗaya daga cikin jagororin da ke kula da filin Sunusi Abdullahi Muhammad, a wani taron manema labarai da su ka gudanar a Kano.

Ya ce duk wata hanya ta cika ƙa'idar mallakar waje sun cika ta amma rana tsaka sai su ka ji malamin na cewa gwamnan Kano ya ba shi gurin, a don haka ba za su lamunta ba.

Shima da yake nasa jawabin Alhaji Shehu Ya'u Fagge, ɗaya daga cikin dattawan da ke kula da wajan, ya ce tun lokacin sarkin Kano Abdullahi Bayero ya mallaka wa M ber Head ɗin zuwa yanzu aƙalla shekaru 70 Kenan.

Dangane da koken na su ne muka tuntubi Malam Tijjani Bala Ƙalarawi, inda ya ce filin ba na kowa ba ne sarkin Kano Alhaji ya bayar ne don kowa ya amfana da shi.

"Tunda aka bayar da gurin ne mu ke koyar wa a cikin filin, kuma daga bisani Gwamnan jihar Kano, ya mallaka mana gurin domin ci gaba da hidimtawa al'umma, in ji shi.”

Wakilinmu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, yanzu haka al'umma da dama na amfani da wajan domin harkokin su na yau da kullum.

Ready to PlayDala FM88.5 FM