Shugaba Tinubu ya aike da sunan Joseph Tegbe ga Majalisa don tantance shi a matsayin Ministan Lantarki

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan Mista Joseph Olasunkanmi Tegbe zuwa Majalisar Dattawa, domin tabbatar da shi a matsayin sabon Ministan wutar Lantarki a Najeriya.
Wannan na cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, 2026.
Sanarwar ta ce naɗin na Tegbe ya biyo bayan murabus ɗin da tsohon Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ya yi, domin tsayawa takara a zaɓen 2027.
Waye Joseph Tegbe?
Tegbe, ɗan asalin Jihar Oyo ne, ƙwararre ne a fannin tattalin arziki da gyaran kasafi, inda yake da gogewar aiki ta shekaru sama da 35 a sassa daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu.
Kafin wannan naɗi, shi ne Babban Darakta kuma Jami'in Hulɗa na haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da ƙasar Sin (NCSP), inda yake kula da ƙarfafa dangantakar ci gaba tsakanin ƙasashen biyu. Haka kuma, ya taɓa zama babban abokin tarayya a shahararren kamfanin nan na KPMG reshen Afirka.
Tegbe ba baƙo ba ne a fannin lantarki, domin ya yi ayyuka da dama da suka shafi gyara a hukumomi irin su Hukumar Lura da Ma’aikatan Lantarki (NERC) da Kamfanin Sayen Lantarki na Ƙasa (NBET).
Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa Tegbe zai yi amfani da dumbin gogewarsa wajen kawo sauye-sauye masu ma'ana a fannin wutar lantarki, da tabbatar da dorewar samar da wutar, da kuma jawo masu zuba jari kamar yadda kundin manufofin 'Renewed Hope' ya tanada.
A halin yanzu dai, ana jiran majalisar dattawa ta tantance shi kafin rantsar da shi domin fara aiki gadan-gadan.



