Hukumar Hisbah ta ƙaddamar da Form ɗin auren gata na zawarawa a Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ƙaddamar da Form ɗin shirin auren gata da gwamnatin Kano za ta yi wa zawarawa a faɗin jihar.
Wannan na cikin jawabin da kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Birnin Kano Hamidan Tanko Alasaka, ya yi wa kafar Arewa Updates a ranar Laraba 29 ga Afrilun 2026.
Alasaka ya ce, an bai wa dukkan kwamandojin Hisbah na ƙananan hukumomi 44 da ke jihar Fom din yankunansu, domin su kai wa shugabannin ƙananan hukumominsu don fara rabawa waɗanda suka dace.
Dangane da masu buƙatar fom ɗin kuwa, Kwamandan ya ce, su saurari sanarwa ta gaba daga hukumar domin sanin yadda za a karba tare da ka’idojin auren da aka shinfiɗa.



