Gwamnan Kano zai binciki, tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a wawure kuɗin ma'aikatan Kano Naira biliyan 1.5

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce za a yi bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen wawure kuɗaɗen ma'aikatan jihar Naira biliyan 1.5
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan da Shugaban ƙungiyar ƙwadago na Kano, Kwamared Kabiru Inuwa ya yi ƙorafi kan wasu kalamai da kwamishinan yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi, da suka zargi tsohon Shugaban ma'aikatan jihar Abdullahi Musa da yin almundanar kudin wadanda yawan su ya kai naira biliyan 1.5.
Wannan dai na zuwa ne a wani ɓangare na bikin ranar Ma'aikata ta Duniya da ake gudanar wa a yau, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware 1 ga watan Mayun kowacce shekara, domin gudanar da bikin ranar.
A jihar Kano ma, gwamnatin jihar ta jagoranci ƙungiyoyin Ma'aikata inda aka gudanar da bikin ranar a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata, wanda ma'aikata da ƴan siyasa da dama suka samu damar halarta.



