Ranar ma'aikata: Rana ce ta ƙalubale ga ma'aikata a Najeriya - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Center for Human Rights and Charity Development initiatives, ta ƙalubalanci gwamnatin tarayya kan yadda ma'aikata ke fuskanta ƙalubale a ɓangaren al'amuran more rayuwa da ƙarancin kyautata musu.
Babban Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Kwamared Dr. Auwal Jibril Maifada, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Juma'a 1 ga watan Mayu, 2026.
Dr. Auwal Maifada, na wannan bayanin ne a wani ɓangare na bikin ranar Ma'aikata ta duniya da ake gudanar wa a yau, inda Majalisar ɗinkin Duniya ta ware 1 ga watan Mayu na kowacce Shekara domin gudanar da bikin ranar.
A ɓangaren kula da walwala, da isasshen albashi, da kuma dukkanin wani abu na kyautata wa ma'aikata, Dr. Auwal Maifada ya ce akwai ƙarancin hakan daga gwamnatocin ƙasar al'amarin da ke ƙara tagayyara rayuwar ma'aikata.
A cewar sa, "Abin takaici ne yadda mafi yawan ma'aikata ke fuskantar ƙalubale ta ɓangarori daban-daban, al'amarin da ke kawo tazgaro ga rayuwar su da ma aikin da suke yi," in ji shi.
Dr. Auwal ya kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta sauƙaƙa wajen ɗai-ɗaita farashin kayayyakin masarufi da na amfanin yau da kullum, domin ma'aikatan su samu sauƙi.
Ya kuma ce akwai buƙatar gwamnati ta ƙara duba a kan hanzarin shigar da bayanan ma'aikaci da zarar an yi masa ƙarin girma, tare da duba a kan jinkirin fitar kuɗin hutun su domin inganta rayuwar su.
A cewar sa, "A mafi yawan lokuta sai ma'aikaci ya samu ƙarin girma amma sai ya samu tsawon wasu lokuta na tare da an shigar masa ba, lamarin da ke damum ma'aikaci," in ji Auwal Maifada.



