Koma Labarai
Tsaro

Rundunar Anti-Phone Snaching force ta cafke matasa 3 kan satarwa mai adai-daita sahu waya a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar Anti-Phone Snaching force ta cafke matasa 3 kan satarwa mai adai-daita sahu waya a Kano.

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile sha da dillancin kayan maye, ta Anti - illicit drugs/Phone Snaching force a Kano, ta cafke matasa uku a yankin Ja'en bisa zargin su da yi wa wani mai baburin adai-daita sahu satar waya.

Mai magana da yawun rundunar tsaron Ibrahim Garba Ahmad ne ya bayyana wa Dala FM kama matasan uku a ranar Laraba 21 ga watan Oktoba, 2026.

Ya ce hakan na zuwa ne bayan da suka samu bayanan sirri ne a kan yadda matasan ke yawan yi wa masu baburan adai-daita sahu dabaru suna satar musu kuɗaɗe da wayoyi idan sun tsayar da su a matsayin fasinja a yankin Ja'en.

A cewar sa, bayan samun ƙorafin ne Kwamandan rundunar tsaron ta Anti-illicit drugs/Phone Snaching force, Nura Salisu Sharaɗa, ya tura jami'an su na farin kaya yankin, domin kamo matasan da ake zargi da wannan aika-aikar.

Ibrahim Garba, ya kuma ce, bayan da wasu matasa suka zare wayar wani mai baburin adai-daita sahu ne a yankin Ja'en layin gidan dagaci, jami'ansu suka cafko matasa uku, tare da kamo matashin da ya sayi wayar da suka sata.

Matasan da ake zargi da satar wayar sun ce suna tare mai baburin adai-daita sahu ne sai su rabu, wasu ta wajen direban, wani kuma ya zagaya da gefen sa ya satar masa kuɗi ko waya a wajen da ake ajiye kuɗin ciniki.

Sai dai matasan mazauna unguwar Ja'en sun bayyana nadamar su, inda suka ce ba za a ƙara samun su a cikin wannan mummunar ta'ada ba.

Shima matashin da ya sayi wayar da ake zargin matasan sun sato, ya ce ya sayi wayar a wajen matasan ne ba tare da yasan ta sata ce ba, domin sai da wani ya tsaya musu ma sannan ya saya.

A cewar sa, "Inda nasan wayar ta sata ce da ba zan saya ba domin a tsarin sana'ata ta waya bana sayen wayar sata ko kuma sayan wayar da babu kwali ko rasit, amma zan ƙara kiyaye wa," in ji shi.

Daga bisani Kakakin rundunar tsaron ta Anti-illicit drugs/Phone Snaching force a nan Kano, Ibrahim Garba Ahmad, ya ce da zarar sun kammala bincike za su miƙa matasan inda ya dace domin ɗaukar mataki na gaba a kan su.

Ya kuma gargaɗi dukkan ɓata garin da ke addabar mutane da aikata miyagun laifuka da su daina, yana mai cewa ba za su saurara wa duk wanda suka kama da aikata laifuka ba.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM