Jami'in Karotar da ya samu karaya 6 a sassan jikin sa bayan ture shi da wani mai mota ya yi a Kano, ya rasu.

Rahotannin da ke fitowa na bayyana cewa, jami'in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, Nasiru Abdullahi, wanda akafi sani da Baba Nasiru, ya rasu, bayan da wani direba ya ture shi inda ya samu karaya guda 6 a sassan jikin sa.
A kwanakin baya ne dai ɗan Karotan da akafi sani da suna Baba Nasiru, ya samu karaya 6 a sassan jikin sa bayan da wani Direban mota ya kaɗe shi da Mota, ya gudu a Dambatta, inda aka ka shi Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed, da ke birnin Kano.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin sanarwar da mataimaki na musamman ga Shugaban Hukumar Karota a kafafen sada zumunta, Mu'azzam Mansur Kurawaz ya fitar a ranar Juma'a 04 ga watan Satumba, 2026.
Ya ce Marigayin ya rasu ne a wannan rana ta Juma'a 4 ga watan Satumba, 2026, a Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed.
A cewar Kurawa, bayanin rasuwar jami'in hukumar Karotan, ta fito ne ta hannun Shugaban hukumar Shiyyar Dambatta OC Ali Mustapha Rabatsu.
Sanarwar ta ce yanzu haka ana kan yin jana'izar Marigayin a Garin Ɗanbatta, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.



