Ƙu ƙara haɗa kan ku don ciyar da al'umma gaba tare da magance matsalolin tsaro - Sarkin Gaya

Mai martaba Sarkin Gaya, Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Gaya, ya buƙaci al'ummar unguwannin Ɗorayi da kewaye, da su ƙara haɗa kan su, tare da rungumar zaman lafiya, domin ci gaban jama'a a yankin da ma jihar Kano baki ɗaya.
Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin da Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, haɗin gwiwa da Kwamitin tsaro na unguwannin Ɗorayi da kewaye, suka ziyarce shi a ranar Lahadi 23 ga watan Agustan 2026, tare da karrama shi da shaidar girmama wa, a gidan sa da ke yankin Ɗorayi.
Dr. Aliyu Ibrahim ya kuma ce, akwai buƙatar Gamayyar Matasan da ƴan kwamitin tsaron na Unguwanni Ɗorayi, su ƙara bada dukkan gudunmawar su wajen ganin an ƙara daƙile matsalolin tsaro tare da wanzuwar zaman lafiya a sassan jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.
Da yake nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, Alhaji Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ya ce sun karrama Sarkin ne bisa irin ƙoƙarin sa a harkar tsaro, da kuma samar da ci gaban al'umma.
Ya kuma ce a shirye suke wajen ci gaba da bada dukkan gudunmawar su a harkar tsaro da ma sauran ɓangarori, domin ganin an ƙara daƙile matsalar tsaron a faɗin jihar Kano.
Shima a nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin tsaro na unguwannin Ɗorayi da kewaye, Mallam Abdullahi Idris Ɗan Fodiyo, ya ce ƙoƙarin da Sarkin yake yi a ɓangarori daban-daban na al'umma ne ya sa suka ga dacewar su yaba masa ta hanyar karrama shi.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da Kwamishinan ƴan sandan jihar nan, da su yi wa Allah, su mayar da ofishin ƴan sanda na SWAT, da ke Ɗorayi, zuwa Division, domin sai ya fi yi wa al'ummar yankin amfani.
Haka kuma, Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, ta karrama Mai unguwar Chiranchi Gabas Mallam Shehu Iliyasu, ta hannun Mai martaba Sarkin Gaya Dr Aliyu Ibrahim, bisa irin ƙokarin da yake yi wajen samar da ci gaban al'ummar sa.



