Hukumar yaɗa ilimin Manya ta jagoranci tallafawa yara masu talla 100, da jarin kuɗi a Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Hukumar yaɗa ilimin Manya ta jihar Kano, wato Agency for Mass Education, ta jagoranci tallafawa yara masu talla, sama da su 100, da jarin kuɗi domin inganta sana'arsu a unguwar Ajawa Saberi da ke yankin Ja'en a ƙaramar hukumar Gwale da ke jihar Kano.
Shugabar hukumar Dr. Binta Abubakar, ce ta jagoranci tallafawa wa yaran a ranar Alhamis 18 ga Yuni, 2026.
Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa, Dr. Binta ta kuma ce an tallafawa yaran ne a ƙokarin hukumar na cigaba da ilimantarwa, tare da tallafawa yara masu talla, domin inganta sana'ar tasu da ma rayuwar su baki ɗaya.
A yayin taron, yaran da aka tallawa sun nuna farin cikin su tare da shan alwashin yin abinda ya dace a harkar sana'ar da suke yi.



