Koma Labarai
Labarai

Matasan Dakata sun gudanar da tattakin lumana don neman a gyara titin Kwanar Kotu zuwa ofishin Ƴansandan yankin a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Matasan Dakata sun gudanar da tattakin lumana don neman a gyara titin Kwanar Kotu zuwa ofishin Ƴansandan yankin a Kano

Wasu matasa mazauna unguwar Dakata a ƙaramar hukumar Nassarawa ta jihar Kano, sun gudanar da tattakin lumana domin jan hankalin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki, kan buƙatar gaggauta gyaran titin Kwanar Kotu zuwa ofishin Ƴan Sanda na Dakata.

Matasan sun bayyana cewa sun fito ne domin isar da kukansu cikin lumana, sakamakon mummunan halin da titin ke ciki, wanda suka ce ya jima yana jefa al'umma cikin wahalhalu tare da kawo cikas ga zirga-zirga da harkokin yau da kullum.

A cewarsu, "Lalacewar titin na haifar da matsaloli da dama ga mazauna yankin da masu amfani da shi, lamarin da ya sa suka nemi gwamnati da sauran hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakin gaggawa domin gyara titin.

Sun kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su saurari koken al'ummar Dakata tare da yin duk mai yiwuwa wajen magance matsalar, domin sauƙaƙa zirga-zirga da inganta rayuwar mazauna yankin.

Matasan sun jaddada cewa tattakin da suka gudanar na lumana ne, kuma manufarsa ita ce isar da saƙon al'umma cikin kwanciyar hankali, ba tare da tayar da wata fitina ko hargitsi ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM