NDLEA ta cafke mutane 73 da ake zargi da ta'ammali da ƙwayoyi a Kano

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta cafke aƙalla mutane 73, waɗanda ake zargin su da aikata laifuka masu alaƙa da ta'ammali da ƙwayoyi a jihar.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa wannan na cikin sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Sadik Muhammad Mai Gatari, ya fitar ga manema labarai, a ranar Alhamis 11 ga Yuni, 2026.
Ya ce wannan na zuwa ne biyo bayan sumamen da jami'an hukumar suka gudanar na kwana ɗaya, inda take zargin su da laifuka masu alaƙa da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar Kano.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar ta ƙara matsa lamba wajen kai sumame guraren da ake dillanci, da kuma ta'ammali da kayan maye a sassan jihar Kano, inda take kama su tare da miƙa su gaba.
Jihar Kano dai na daga cikin jahohi da wasu matasa ke ta'ammali da kayan maye, da faɗan daba da kuma ƙwacen waya, ko da ike hukumomin tsaro tuni suka bayyana cewa sun tashi tsaye don kawo ƙarshen matsalolin a jihar.



