Koma Labarai
Shari'a

Matar da ake zargin ta kashe mijinta kan hana ta zuwa gidan biki ta ƙara gurfana a gaban kotu a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Matar da ake zargin ta kashe mijinta kan hana ta zuwa gidan biki ta ƙara gurfana a gaban kotu a Kano.

Kotun Majistret mai lamba 9 karkashin jagorancin mai shari'a Haulatu Magaji Kankarofi, ta sake aikewa da wata mata gidan gyaran hali bisa zargin aikata laifi.

Tunda fari dai Ƴan Sanda ne suka gurfanar da matar wadda ake zargi da laifin kashe mijinta ta hanyar caka masa wuka a ƙirji.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar matar mai suna Khadija Sa,idu Hayin Lawali, ta samu saɓani da mai gidanta lokacin da ta tambaye shi zuwa gidan biki sai ya hana ta sakamakon ruwan sama daga nan aka yi zargin ta soka masa wuƙa a ƙirji yana tsaka da yin barci a kan doguwar kujera.

A zaman kotun na yau, mai shari'a Haulatu ta bayyana cewar, ana jiran shawarar lauyoyin gwamnati domin ɗaukar mataki na gaba.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa mai gabatar da ƙara ta bayyana wa kotun cewar likitocin asibitin Murtala sun tabbatar da rasuwar Mallam Auwal Adam mijin matar kotun ta sanya ranar 18 ga wannan watan dan a ƙara gabatar da ita.

Ready to PlayDala FM88.5 FM