Mutane 53,000, ne ke mutuwa duk shekara bisa cin gurbataccen abinci a Nijeriya - Gwamnatin Tarayya
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ce, sama da mutane 53,000 ne ke mutuwa, yayin da kusan miliyan 50 ke kamuwa da cututtuka a duk shekara sakamakon cin gurbataccen abinci a Najeriya.
Karamin Ministan lafiya da Jin dadin jama'a, Dakta Iziaq Salako ne ya bayyana hakan a Abuja, a yayin taron manema labarai na bikin Ranar Tsaron Abinci ta Duniya ta 2026, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da masana ke ta kira ga al'umma da su rinƙa ƙauracewa cin gurɓataccen abinci domin kula da lafiyar su.



