Koma Labarai
Tsaro

Civil Defense ta kori jami'an ta na sa-kai guda biyar a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Civil Defense ta kori jami'an ta na sa-kai guda biyar a Kano

Rundunar tsaron al'umma ta ƙasa Civil Defence, reshen Jihar Kano, ta kori jami’an ta na sa-kai su biyar daga bakin aiki, bisa zargin su da laifin rashin ɗa’a, da rashin ƙwarewa da kuma karya ƙa’idojin aiki.

Kwamandan rundunar ta Civil Defense a nan Kano, Mohammed Hassan Agalama, ne ya bayar da umarnin korar jami'an na sa-kai, inda ya ce an amince da korar tasu ne bayan an tabbatar da cewa halayensu sun saɓa da ƙa’idoji da ɗabi’un aikin.

Jami’an da aka kora ɗin sun haɗar da Yakubu Mubarak Yusuf, da Isma’il Muhammad, da kuma Adamu Auwalu, sai Abdulrazaq Suleiman da Ahmad Sarki.

Cikin sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ta Civil Defense ta jihar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi ya fitar, ta ce an kuma ƙwace dukkan kayan aiki da katunan shaidar da korarrun jami'an suke amfani da su, tare da umartar jami’anta a faɗin jihar da ka da su sake amincewa da waɗanda aka kora ɗin a kowane aiki a madadin rundunar.

Da yake yi wa Dala FM ƙarin bayani game da korar jami'an, SC Ibrahim Idris Abdullahi ya ce, rundunar ta jaddada cewa ba za ta lamunci rashin ɗa’a ba, kuma duk wanda aka samu da laifin ɓata sunanta zai fuskanci hukuncin da ya dace, shi ya sa ma aka buga misali da mutane biyar ɗin.

Da suke zantawa da manema labarai, biyu daga cikin jami'an sa kai ɗin da rundunar Civil Defense ɗin ta kora, sun magantu, inda suka ce sun karɓi ƙaddarar da ta same su.

Tuni dai rundunar ta karbe dukkanin wata shaida ta aiki daga hannun mutane biyar ɗin da ya kora, tare da gargaɗin ka da su sake kiran kansu a matsayin jami'anta.

Ready to PlayDala FM88.5 FM