Koma Labarai
Labarai

Karota ta tura Ma’aikata 1,000 sassan Kano don shirye-shiryen bukukuwan Babbar Sallah

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Karota ta tura Ma’aikata 1,000 sassan Kano don shirye-shiryen bukukuwan Babbar Sallah

Hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta sanar da tura ma’aikatan ta 1,000 zuwa muhimman gurare a sassan jihar, domin shirye-shiryen karɓar bukukuwan Babbar Sallah, (Eid-Kabir) da ke tafe.

Tashar Dala FM Kano, ta ruwaito cewa wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Abubakar Ibrahim Sharaɗa, ya fitar a ranar Litinin 25 ga Mayu, 2026.

Sanarwar ta ce wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren da hukumar ta ɗauka, domin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa cikin sauƙi tare da kiyaye doka da oda a lokacin bukukuwan.

"Za a jibge ma’aikatan Karota a wurare masu muhimmanci da suka haɗa da filayen sallar Idi, da manyan tituna, da kuma wuraren shaƙatawa inda ake sa ran taruruwar jama’a, in ji Abubakar.”

Sanarwar ta kuma ce, Manajan Injiniya Darakta na KAROTA, Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana cewa hukumar na nan daram wajen kare lafiyar masu amfani da hanya da kuma rage cunkoson ababen hawa a lokacin bikin.

Ya kuma yi kira ga direbobi da sauran masu amfani da tituna da su baiwa jami’an Karota haɗin kai tare da bin dokokin hanya yadda ya kamata, don tabbatar da gudanar da bukukuwan Sallar cikin lumana ba tare da wata matsala ba.

A nasa jawabin, Shugaban Sashen Ayyuka na KAROTA, Auwal Shehu Muhammad (Kofar Mata), ya ce Manajan Daraktan hukumar na yi wa daukacin al’ummar jihar fatan samun Sallah cikin kwanciyar hankali da tsaro.

Ready to PlayDala FM88.5 FM