An tantance mutane 720, waɗanda ke neman gurbi a auren gata na gwamnatin Kano - Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce zuwa yanzu an tantance aƙalla mutane 720, maza da mata, waɗanda ke neman gurbi a tsarin auren gata da gwamnatin Kano, za ta yi wa aƙalla mutane dubu uku a jihar.
Mataimakin Babban Kwamandan hukumar a Kano, Dr. Mujahideen Aminudden Abubakar, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Dala FM a ranar Laraba 10 ga Yuni, 2026.
Ya kuma ce waɗanda aka tantance ɗin sun fito ne daga ƙananan hukumomin wajen Kano 24.
Har ila yau, hukumar Hisbar ta buƙaci waɗanda suka cike Fom, ɗin neman gurbin auren gatan na hedikwatar hukumar, su je ofishin SAKA, da form ɗin su, da kuma gwajin da suka yi domin a ci gaba da tantance wa.
A cewar sa, za su je ne a yau Laraba 10 ga Yuni, 2026, inda ya ce ragowar ƙananan hukumomin da ba a tantance ba, za su ji ranar da za a tantance su nan ba da jimawa ba.



