Za mu faɗaɗa noman rani da ban ruwa na zamani don rage tsadar rayuwa a Najeriya - Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta faɗaɗa noman rani da ban ruwa na zamani domin rage tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar ga ƴan Najeriya a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Shugaban ƙasar ya kuma ce, rage tsadar rayuwa na cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta bai wa fifiko, inda za ta yi ƙoƙarin rage kuɗin samarwa da jigilar kayayyakin da ’yan Najeriya ke amfani da su.
Ya ce gwamnati za ta faɗaɗa noman rani da ban ruwa na zamani, inganta samun iri da taki, ƙara amfani da injuna wajen noma tare da zuba jari da adana amfanin gona da kuma sufuri.
A cewar sa, "Mu na gina da kammala hanyoyi, layukan dogo da tashoshin jiragen ruwa da za su haɗa gonaki da masana’antu da kasuwanni," in ji shi.
Tinubu ya ƙara da cewa rage kuɗin noma da asarar amfanin gona kafin isa kasuwa zai taimaka wajen rage farashin kayayyaki.



