Koma Labarai
Tsaro

An ƙaddamar da Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa don tunkarar matsalolin yankin.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An ƙaddamar da Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa don tunkarar matsalolin yankin.

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewacin Najeriya, ta buƙaci shugabannin Arewa da su ƙara tashi tsaye, domin ganin an ƙara daƙile matsalolin tsaro a yankin.

Shugaban ƙungiyar Muhammad Tijjani Ɗorayi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Kano, jim kaɗan bayan ƙaddamar da ƙungiyar.

Muhammad Tijjani ya ce manufar ƙungiyar ita ce, yadda za su tunkari yadda arewa ke fuskantar matsaloli musamman na tsaro, da lokaci yayi da al'ummar wannan yanki za su fito don kawo ƙarshen su, ta hanyar fitowa su zaɓi cancanta a lokacin zaɓe.

Sai dai MTD, ya ce, ƙungiyar ta lura da cewa yanzu an fara samun nasara wajen yaƙi da ta'addanci a sassan Najeriya, la'akari da yadda hukumomin tsaro ke ƙara ƙarfafa tsaro a ƙasar.

A cewar sa, "Domin ganin an ƙara daƙile sauran matsalolin tsaro a yankin Arewa, ya sa ƙungiyar mu ta kai takardu ofishin Ministan tsaro Christopher Musa, don ganin an yi abinda ya dace wajen magance matsalar," in ji MTD.

Ya kuma ce yanzu haka sun shirya tunkarar dukkan ministocin tsaro, mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaro NSA, Nura Ribaɗo, da sauran shugabannin Arewacin Najeriya, domin ganin an lalubo hanyoyin daƙile matsalolin tsaro a Arewa.

Muhammad Tijjani Ɗorayi ya ƙara da cewa, yanzu haka ta ƙudiri aniyar gudanar da gangamin wayar da kan matasa, don ganin sun kaucewa shiga bangar siyasa da shaye-shaye a yayin babban zaɓen 2027.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM