Koma Labarai
Labarai

An hana kai kayan lefe da jerin gwanon motoci lokacin kai amarya a yankin Gwuiwa na jihar Sokoto

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An hana kai kayan lefe da jerin gwanon motoci lokacin kai amarya a yankin Gwuiwa na jihar Sokoto

Mahukuntan yankin Guiwa da ke Ƙaramar Hukumar Wamako a Jihar Sokoto sun sanar da sabbin dokoki da suka haramta wasu al’adun aure domin rage tsadar aure da sauƙaƙa wa matasa damar yin aure.

Sarkin Kudun Guiwa, Alhaji Muhammad Mode Guiwa, ya bayyana cewa daga yanzu an haramta kayan lefe, kayan I See I Love, jerin gwanon motoci yayin ɗaukar amarya da wasu al’adun bukukuwan aure.

Ya ce maimakon kayan lefe da na I See I Love, an amince da kwando guda ɗaya da kuma sadaki.

Sabbin dokokin sun kuma haramta kaɗe-kaɗen wazigidi, kauyawa, kamun amarya, haɗuwar maza da mata a wuraren bukukuwan aure, tare da takaita motocin da za su raka amarya zuwa biyu kacal.

Haka kuma, an haramta gayyatar Fulani daga waje domin halartar bukukuwan aure, tare da hana saye da sayar da miyagun ƙwayoyi a wuraren bukukuwa.

Sarkin Kudun ya ce duk wanda ya karya waɗannan dokoki zai fuskanci hukunci, inda za a yi amfani da jami’an ’yan sanda, Civil Defence, Hisbah da ’yan banga wajen tabbatar da bin su.

Ready to PlayDala FM88.5 FM